Ranar MƊD ta Duniya: Babban Jami’in MƊD a Nijeriya, Matthias Schmale ya yi wa ƙasar saƙo mai ratsa jiki

Babban Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mista Matthias Schmale, ya gabatar da jawabi mai ratsa jiki domin bikin ranar Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda ake gudanarwa kowace shekara don tunawa da muhimmiyar ranar da Yarjejeniyar Kafa Majalisar Ɗinkin Duniya ta fara aiki a ranar 24 ga Oktoba,1945.

A jawabin nasa, babban jami’in ya yi tsokaci a kan ƙa’idoji da ayyukan MƊD da kuma ƙalubalen da duniya ke fuskanta a yau.

Mr. Schmale ya fara ne da taɓo batun yadda aka buɗe taron Yarjejeniyar Kafa MƊD, wanda ya jaddada cewa babban ƙudirin kafa hukumar shi ne “ceto al’ummar duniya daga bala’in yaƙi.”

Ya ce a shekarar 2023, wannan ƙudiri na fuskantar ƙalubalen da ba a taɓa ganin irinsa ba, inda tashe-tashen hankula suka shafi miliyoyin mutane a wurare kamar Ukraine, Falasɗinu, Isra’ila, Sudan da Myanmar da kuma korar shugaban Nijar da aka yi a kwanan baya.

Babban Jami’in ya buƙaci ƙasashen ƙungiyar su sake jaddada sadaukarwarsu da girmama Yarjejeniyar ta Majalisar Ɗinkin Duniya, da kuma sabunta ƙoƙarinsu na inganta zaman lafiya, yana mai bayyana cewa, wannan shi ne muhimmin saƙon Babban Sakataren MƊD, Antonio Guterres a bana.

Ya kuma yaba wa ma’aikatan MƊD Nijeriya waɗanda suke aiki ba tare da gajiya ba, a lokuta da dama a cikin mawuyacin hali, domin cika burin Majalisar Ɗinkin Duniya na samar da zaman lafiya da wadata ga kowa da kowa.

Ya kuma tuna tare da bayyana alhini kan ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya guda 23 da suka rasa rayukansu a harin ta’addancin da aka kai a ofishin MƊD da ke Abuja a shekarar 2011 da kuma abokan aikinsu da ke ci gaba da sadaukarwa a yanayi na tashe-tashen hankula.

Mr. Schmale ya kuma bayyana kudira MƊD kan cimma ajandar 2030 da kuma manufofin ci gaban zamani masu ɗorewa (SDGs), tare da jaddada ƙa’idar kowa ya bayar da gudunmawa a dama da shi ba tare da barin kowa a baya ba.

Ya yi alƙawarin mayar da hankali wajen magance matsalolin da suka shafi yara da ba su zuwa makaranta, rashin abinci mai gina jiki, cin zarafin mata da ‘yan mata, da buƙatun al’umma masu rauni da suka haɗa da tsofaffi, nakasassu, da ‘yan gudun hijira.

Har ila yau, ya yi kira ga shugabannin gwamnati da su hanzarta aiwatar da ajandar 2030 sannan ya yi magana game da ɗimbin damar da Nijeriya ke da ita ta bunƙasa da ciyar da kanta gaba, yana mai jaddada buƙatar mayar da hankali wajen aiwatar da lamarin bilhaƙƙi.

Bikin na bana mai taken, “Haɗin Gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya tare da Nijeriya don Cimma Tsarin SDGs,” ya mayar da hankali ne a kan bayyana mahimmancin haɗin gwiwa da sauke nauyin da ke wuyar juna.

Babban Jami’in ya jaddada ƙoƙarin da majalisar ke yi na kara samun kayan aiki don magance matsalolin kiwon lafiya kamar cuta mai karya garkuwar jiki (AIDS), da tarin fuka, da zazzaɓin cizon sauro, da kuma tallafa wa samar da zaman lafiya, magance rikice-rikice, da inganta hanyoyin sa ido ga rundunar ‘yan sandan Nijeriya.

Bugu da ƙari, ya amince da ayyukan jin kai a jihohin Borno, Adamawa, da Yobe, inda aka bayar da agajin gaggawa ga marasa galihu miliyan 3.6 a farkon rabin shekarar nan.

Mr. Schmale ya kuma tunatar da kowa da kowa cewa dole ne dukkanin ayyukan ci gaba su kasance daga tushe a cikin mutunta haƙƙin ɗan’adam, bayar da shawarar ‘yancin fadin albarkacin baki, da kuma daƙile kalaman ɓatanci da kiyayya.

Mr Schmale ya kammala jawabinsa da neman haɗin kai da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, ƙungiyoyin fararen hula, ɓangarori masu zaman kansu, da kafafen yada labarai wajen tabbatar da akidu da ganin kimar MƊD don ci gaban mutanen duniya da samun wadata, da zaman lafiya.