Shugaban INEC ya gana da jam’iyyun siyasa gabanin zaɓen gwamnoni a jihohin Kogi, Bayelsa, Imo

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Mahmood Yakubu, ya gana da shugabannin jam’iyyun siyasa a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Talata.

Taron ɓangare na shirye-shiryen da INEC ke yi don gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohin Kogi da Bayelsa da kuma Imo nan gaba kaɗan.

Ana sa sa ran shugaban INEC ya yi wa jam’iyyun bayanin shirye-shiryen INEC kan zaɓuɓɓukan da kuma rawar da Jam’iyyun za su taka.

Kazalika, taron wata dama ce ga jam’yyun da lamarin ya shafa su bayyana wa shugban INEC damuwarsu da sauran lamurran da suka yi la’akari da su gabanin zaɓen.