Na san talakawan Nijeriya na shan wahalar cire tallafin fetur – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA aAbuja

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya fahimci irin wahalhalun da ke tattare da cire tallafin man fetur, yana mai tabbatar da cewa matakin na da amfani ga ƙasar nan, musamman wajen tabbatar da ci gaba a nan gaba.

Tinubu, wanda ya karɓi baƙuncin tsoffin gwamnoni 18 da su ka yi gwamna tare a 1999, a fadar shugaban ƙasa, ya roki ‘yan Nijeriya da su ƙara haƙuri.

Ya kuma tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa ana shirin aiwatar da tsarin da zai magance raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Tinubu ya ce gwamnati za ta ƙara ƙoƙari, ta hanzarta aiwatar da samar da tallafi ga ‘yan ƙasa,  musamman tallafin kuɗaɗe, inda ya tabbatar da cewa za a raba tallafi ba tare da almundahana ba.

“Na fahimci cewa mutanenmu suna shan wahala. Kowa ya san ba za a iya haihuwa ba tare da ciwo ba. Murnar haihuwa shine jin daɗin da ke zuwa bayan ciwo. Nijeriya ta riga ta sake haihuwa ta hanyar cire tallafin mai. Wani mataki ne da ‘yan ƙasa mafi rinjaye za su amfana a kan wasu tsirari. Don Allah a gaya wa mutane su ɗan yi haƙuri.”

“Jin daɗi da sauƙi na nan zuwa. Ba na son raba tallafin na kuɗi ya faɗa hannun ‘yan sama da faɗi. Na san matakin akwai raɗaɗi. A ƙarshe, za mu yi murna da ci gaban ƙasarmu,’’ kamar yadda ya shaida wa gwamnonin, waɗanda tsohon Gwamnan Jihar Edo, Lucky Igbinedion ya jagoranta.

Daily Trust ta rawaito cewa tun da fari, Tinubu ya rubutawa majalisar wakilai cewa ya nemi a gyara ƙudurin kasafin kuɗi na 2023 domin fitar da Naira biliyan 500 don samar da ababen more rayuwa ga ‘yan Nijeriya.