HortiNigeria ta gudanar da bita ga manoman Kano

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

A ranar Talatar da ta gaba ta ne ƙungiyar HortiNigeria ta gabatar da taron bita na farko ga manoma a Jihar Kano.

HortiNigeria, wata ƙungiya ce da take tallafa wa manoman lambu da dabarun yadda za su inganta nomansu.

Ƙungiyar, wacce take samun tallafi daga Ƙasar Netherlands, ta qaddamar da aikin ne ta karkashin cibiyar samar da takin zamani ta kasa (IFDC) tare da wasu abokan hurdar su.

A nasa Mohammed Salasi Idris daraktan shirye shirye na Horti Nigeria ya baiyanawa manema labarai cewa wannan shiri ne da gwamnatin netherland ta ɗauki nauyin na tsawon shekara hudu wanda aka fara shi a 2021 da nufin bunƙasa noman kayan lambu a Nigeria, musamman tumatiri, Albasa, Kuɓewa, tattasai, Kabeji, Kokwamba da kankaana. Shirin dai yanzu haka yayi nisa a jahohin Oyo, Ogun, Kano da Kaduna.

Haka shi ma wakilin IFDC/HORTI Nigeria Abdulƙadir Umar ya baiyana cewa wannan wani shiri ne da gwamnatin ƙasar Netherland da Nigeria Suka sa hannu domin tallafawa Manoman kayan lambu su bunkasa harkokin noman su yadda za su samu iri mai kyau da kuma ilmantar da su tare da haɗa su da yan kasuwa musamman kayan gwari da yake da tsautsayi don haka tun kafin ma su noma za a a haɗa su da yan kasuwa domin sanin inda zasu kai bayan sun noma.

Ramlat Umar guda ce daga cikin wadanda suka ci gajiya shirin ta baiyana cewa ta amfana sosai da fasahar da ta koya daga wannan shiri na Horti ta samu canji sosai wajen samun yabanya me kyau haka ta samu alheri sosai a kasuwa.

Tarron dai ya samu halarta mutane daban-daban daga fadin ƙasar nan wanda ya hada da wakilai daga Ma’aikatar Gona ta taraiya da wasu ɗaiɗaikun mutane daga gwamnati da wasu cibiyoyi haɗe da ofishin jakadancin ƙasar Netherlands na Nijeriya.