Na shirya yi wa Nijeriya kowace irin hidima, inji Shugaban AFDB

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB) mai barin gado Akinwumi Adesina, ya ce a shirye yake ya yi wa Nijeriya da Afirka hidima a kowane irin matsayi bayan ya riƙe muƙaminsa a bankin yankin.

Adesina, wanda aka fara zaɓensa a matsayin shugaban bankin AfDB na 8 a ranar 28 ga Mayu, 2015, zai kammala wa’adinsa na biyu a bankin a kashi na biyu na wannan shekara.

Tsohon Ministan Noma, yayin wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Arise, ya ce, “Abin da ke faranta min rai ba komai bane illa ganin rayuwar mutane ta canja. Abin da ke ba ni gamsuwa kenan. A sakamakon haka, zan kasance a shirye don yin hidima a kowane matsayi, a duniya, a Afirka, ko ina, har da ƙasata.”

Da aka tambaye ni game da matakin da zai ɗauka na gaba da kuma ko zai tsaya takarar Shugaban Nijeriya, Adesina ya amsa cewa: “ɗaya daga cikin abubuwan da nake godiya a matsayina na ɗan Nijeriya: shekaru da yawa da suka wuce, lokacin da nake makarantar kammala digiri a Nijeriya, ko bayan haka, na samu damar samun takardar bizar Amurka. An ba ni biza mai girma, kuma zan iya samun zama ɗan aasar Amurka.

“Amma na ƙi shi, ba don ba na son Amurka ba. Yara na Amurkawa ne; can aka haife su. Na tuna gaya wa abokina cewa wannan fasfo ne na Nijeriya, koren fasfo ne, cewa ba zan iya kuma ba zan taɓa sayar da shi da wani abu ba.

A cewarsa, yana farin cikin zmaa ɗan Nijeriya kuma ɗan Afirka.