Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci dukkan ministocin gwamnatinsa da su bayar da cikakken rahoton yadda suke tafiyar da ayyukansu ga ’yan Nijeriya a nan take.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa Mohammed Idris ne ya sanar da umarnin shugaban ƙasar a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata.
Ministan ya ce, rahoton ministocin zai bai wa ‘yan Nijeriya damar sanin abubuwan da gwamnati ta yi da kuma yin tambayoyi kan su.
Akwai ministoci 48 a majalisar ministocin Tinubu. Daga cikin su akwai Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya; Adebayo Adelabu, ministan wutar lantarki; David Umahi, ministan ayyuka, Olubunmi Tunji-Ojo, ministan cikin gida, da dai sauransu.