Na yi zanga-zanga a baya amma ta lumana, inji Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da cewa ya sha shiga cikin masu zanga-zanga daban-daban amma ba ta tashin hankali ba.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi takardar amincewa daga sabon jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills Jr. a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Ya kuma jaddada muhimmancin ɗorewar dimokuraɗiyya a Nijeriya, yana mai cewa zanga-zangar wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya, amma babu wata gwamnati da za ta amince da zanga-zangar da zai iya janyo asarar rayuka da dukiyoyi.

Shugaban ya ce, “Dangartakarmu da Amurka tana da kyau. Mun yi imani da dimokuraɗiyya da ‘yanci. Wasu magabata sun yi aiki tuƙuru a lokacin da muka miƙa mulki ga dimokraɗiyya, kuma muna tunawa da irin su Ambasada Howard Jeter.

“Muna sa ran Nijeriya da Amurka za su cigaba da yin aiki kafaɗa da kafaɗa don faɗaɗa haɗin gwiwa a kan manufofi guda da ɗabi’un dimokraɗiyya.

“A lokacin soji, mun yi ta raɗe-raɗin nuna adawa da mulkin kama-karya, kuma ina cikin ƙungiyar da suka gudanar da zanga-zangar lumana ba tare da yin ɓarna ba. Mun yi aiki tuƙuru don tabbatar da shekaru 25 na mulkin dimokuraɗiyya ba tare da karyewa ba, kuma zan ci gaba da riƙe wannan dimokuraɗiyya.”

Shugaban ya ce kamar yadda ya yi imanin cewa zanga-zangar wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya, “ba za mu taɓa ƙarfafa duk wata zanga-zangar da za ta kai ga lalata rayuka da dukiyoyi ba”.

Da ya ke maraba da amincewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka game da rawar da Nijeriya ke takawa a Nahiyar a matsayin babbar uwar dimokuraɗiyya a Afirka, Shugaba Tinubu ya yi kira ga gwamnatin Amurka da ta ƙara mai da hankali kan Afirka.

“Nijeriya a shirye take ta taka rawarta a matsayinta na dimokuraɗiyya mafi girma a Afirka wanda ta cancanci a yi koyi da ita  sauran ƙasashen Afirka, amma muna buƙatar ƙarin ƙawancen Amurka a nahiyar wanda ke da amfani ga ɓangarorin biyu. Mun yi imani da ‘yanci, kuma muna ba da jagoranci don bunaasa tattalin arzikin Nujeriya,” inji Shugaban.

By ukarofi