Zanga-zanga: Babu abinda ya haɗa ku da harkar farar hula – Effiong ga sojoji

Spread the love

Wani lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam, Inibehe Effiong, ya ce rundunar sojin Nijeriya ba ta da wani hurumi na fitar da sanarwa kan wani lamari na farar hula.

Masanin shari’ar ya ce, babu wanda zai tsorata da barazanar ta su.

Sanarwar ta zo ne bayan hedikwatar tsaro ta gargaɗi masu gangamin zanga-zangar a faɗin ƙasar cewa ba za ta lamunci rashin zaman lafiya ba.

Kamar aka sani, wasu ’yan Nijeriya na shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar wanda aka shirya gudanarwa daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa 10 ga watan Agustan 2024 domin nuna adawa da matsayin rayuwa.

Zanga-zangar mai taken #EndBadGoɓernace, masu shirya zanga-zangar sun koka kan yadda yunwa da hauhawar farashin kayayyaki ke yaɗuwa a ƙasar.

Rundunar sojin, a yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis, ta ce ta gano maƙarƙashiyar da wasu marasa kishin ƙasa suka shirya domin sanye rigar zanga-zanga tare da mayar da ita tashin hankali ta hanyar kai wa ‘yan Nijeriya da ba su ji ba ba su gani ba hari.

Effiong, lauya mai kare haƙƙin ɗan adam, a cikin wani rubutu a kan shafinsa na Ɗ ranar Alhamis, ya ce ya kamata sojoji su tsaya a bariki su kauracewa harkokin siyasa.

Ya ce: “Rundunar sojin Nijeriya ba ta da wani hurmi na fitar da sanarwa kan wani lamari na farar hula.

“Babu wanda zai tsorata da barazanar ku. Sojoji su tsaya a bariki su daina siyasa,” inji shi.

By ukarofi