Yaƙi da yunwa ya fuskanci koma-baya na shekaru 15 – Majalisar Ɗinkin Duniya

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (SOFI) ta ce, cigaban yaƙi da yunwa a duniya ya fuskanci koma-baya a cikin shekaru 15, wanda ya bar kusan mutane miliyan 733 ke fama da yunwa a cikin 2024.

Wannan adadi, ya ce ya yi daidai da ɗaya cikin mutane 11 a duniya da kuma ɗaya a cikin biyar a Afirka, a cewar sabon rahoton Hukumar ta Majalisar Ɗinkin Duniya (SOFI) da aka buga ranar Laraba.

Rahoton na haɗin gwiwa ne na FAO, da asusun bunƙasa noma na ƙasa da ƙasa (IFAD), da asusun kula da ƙananan yara na MDD (UNICEF), da hukumar samar da abinci ta MDD (WFP), da kuma hukumar kula da lafiya ta MDD (WHO).

Tsakanin mutane miliyan 713 zuwa miliyan 757 ne ba su da abinci a cikin 2023, kusan miliyan 152 fiye da na 2019, inji rahoton.

Halin da ake ciki na yanki ya nuna babban bambanci da yunwar da ke ci gaba da ƙaruwa a Afirka, wanda ya shafi kashi 20.4 cikin 100 na yawan jama’a, yayin da ake zaman kwanciyar hankali a Asiya da kashi 8.1 cikin ɗari.

By ukarofi