Jam’iyyun adawa ne suka shirya zanga-zangar matsin rayuwa, inji Wike

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi zargin cewa ‘yan adawa ne suka ɗauki nauyin gudanar da zanga-zangar da aka shirya yi a faɗin aasar.

Wike, wanda ya bayyana hakan bayan duba aikin titin Apo-Karshi a ranar Talata, ya ce matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita ba Shugaba Bola Tinubu ne ya jawo ta ba.

Yayin da yake neman a ƙara haƙuri, Mista Wike ya ce gwamnati mai ci tana tunkarar ƙalubalen da ta gada daga magabata.

“Mu gaya wa kanmu gaskiya mai sauƙi. Idan muna siyasa, a ce muna siyasa; idan muna son mu kasance masu gaskiya ga kanmu, mu kasance masu gaskiya ga kanmu, mu taimaki ƙasarmu.

“ƙasar ta lalace. Kun san cewa ƙasar nan ta ruguje, kuma gwamnati ta zo ta ga abin da za ta iya yi don aƙalla daga inda muke zuwa wani mataki, kuma ka ce sai an yi abin al’ajabi cikin shekara guda,” inji Wike.

By ukarofi