’Yan kasuwa a Tsohuwar Kasuwar Mpape da ke Ƙaramar Hukumar Bwari a Babban Birnin Tarayya Abuja sun kai ƙara ga Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike bisa cigaba da rusa gine-ginen kasuwar da hukumar ke yi.
Masu shagunan da abin ya shafa sun koka da cewa, ayyukan rushe-rushen da Majalisar Ƙaramar Hukumar Yankin Bwari ke aiwatarwa ta hanyar Hukumar Kiyaye Muhalli ta Abuja (AEPB) ta yi sanadiyar salwantar ɗimbin dukiya, asarar rayuka da rusa rayuwar jama’a, ba tare da wani nau’i na diyya ko wani shiri na daban ga ’yan kasuwar da abin ya shafa ba daga gwamnati.
‘Yan kasuwar ta bakin lauyansu, Dokta Sulaiman Usman (SAN) da Life Bencher, a wata takardar koke ga IGP da ministan babban birnin tarayya, ranar 25 ga watan Yuli, 2024, sun nuna rashin amincewarsu da cewa duk da buaatar neman izinin shiga tsakanin a halin yanzu a gaban babbar kotun birnin tarayya Abuja, sashen Bwari, an ci gaba da gudanar da aikin rusau ba tare da ƙaƙƙautawa ba.
Ya ce, rusau ɗin da aka yi ya janyo asarar rayuka, inda ya ce an kori rumfunan kasuwa da shaguna, lamarin da ya janyo hasarar kuɗaɗe masu ɗimbin yawa.
