A na zargin Matawalle da taimaka wa Yahaya Bello wajen tserewa zuwa Nijar

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A na zargin ƙaramin ministan tsaro, Muhammed Bello Matawalle da shirya ficewar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da ake zargi da sama-da-faɗi da dukiyar al’umma daga Nijeriya zuwa Jamhuriyar Nijar da taimakon jami’an tsaro.

Wani ɗan jaridar bincike mai suna Jackson Ude ya faɗi haka ta kafar X a ranar Alhamis.

Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati, EFCC ta na tuhumar Yahaya Bello da aka zarge shi da handame sama da Naira biliyan 80 a lokacin da ya ke gwamnan Kogi inda ya yi ta ƙoƙarin kaucewa kamawa da kuma bincike.

Ɗan jaridar ya ce, wani binciken sirri ya nuna yadda ƙaramin ministan ya shirya wasu jami’an soji su ka taimaka wa tsohon gwamnan ya tsere zuwa Nijar. A ƙalla jami’ai takwas a ke zargi da raka Yahaya Bello ta ƙaramar hukumar Illela na jihar Kebbi da ke kan iyaka ta amfani da motoci ƙirar ‘Hilux’ guda biyu da kuma wata ‘Land Cruiser’ a yayin ficewar, inji Ude.

Bugu da ƙari, Ude ya shigo da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i inda ya zarge shi da sanya hannu a cikin tserewar Yahaya Bello.

By Babaji