Shugaban ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo ya rasu

Spread the love

Shugaban Ohanaeze Ndigbo, Emmanuel Inwuanyanwu ya rasu. Sanarwar ta fito daga bakin ɗan sa, Jude Inwuanyanwu inda ya ke cewa
” a madadin iyalan Inwuanyanwu, na Umoahii Atta da ke ƙaramar hukumar Ikeduru a Jihar Imo, muna sanar da mutuwar shugaban mu, baban mu, kuma jagora, Eng Emmanuel Inwuanyanwu”

Inwuanyanwu ya rasu ne ranar Alhamis, 25 ga watan Yuli bayan wata gajeruwar rashin lafiya. Kafin mutuwar tashi, shine shugaban ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo.

Inwuanyanwu jagora ne da ke faɗa a ji a yankin nasu, kuma babban ɗan kasuwa ne, kuma mai mallakin sananniyar jaridar nan ta Champion Newspaper.

By ukarofi