DUK da ce-ce-ku-ce tsakanin matatar Dangote da hukumomin kula da harkokin matatar man fetur ta Najeriya, a ƙarshe, Midoil Refining and Petrochemicals Company Limited ya samu damar gudanar da bikin ƙaddamarwa, wanda yake nuni da fara ayyukan ginin matatar a jijar Legas.
An gudanar da bikin ƙaddamarwan ne a Shekungba, a karamar hukumar Ikosi/Ejinrin da ke jihar Legas kwanan nan.
Shugabar kamfanin na Midoil, Mrs Elizabeth-Omolara Akintonde, ta jagoranci manyan mutane zuwa ga filin gurin, wanda ya ratsa al’ummomi da dama a karamar hukumar Ikosi/Ejinrin.
Akintonde ta tabbatar wa shugabanni da al’ummomin cewa matatar man za ta kawo sauyi a yankunansu ta hanyar kawo ci gaba cikin gaggawa, da samar da ayyukan yi ta hanyoyi daban-daban.
Ta yaba wa hakiman kauyukan bisa watsi da suka yi da wasu mutane da suka so su zugasu don su janye amincewar da suka yi da aikin.
Akintonde, wacce cikarra shekaru 74 a duniya ya zo daidai da bikin ƙaddamarwar, ta bayyana cewa matatar ta Midoil za ta kara habaka fannin makamashin Najeriya da karfin tace ganga 100,000 a kowace rana.
Akintonde ta ce, “Duk wadannan duzuzzukan da kuke gani a yau, nan da watanni biyu masu zuwa, ba za ku sake ganinsu ba,” in ji Akintonde, tana mai tabbatar wa mutanen kudurinta na ganin aikin ya tabbata.
Daya daga cikin Daraktocin Midoil kuma shugabar rukunin gidaje na Serenecity Staff Housing, Hajia Amina Abdullahi, ta bayyana farin cikinta kan fara aikin, bayan jinkirin fiye da shekaru goma.
“Mun yi imani da Allah cewa za mu shaida kaddamar da matatar. Mun san cewa wannan babban aiki ne da zai bi ta matakai da yawa, amma da wannan bikin ƙaddamarwar a yau, mun dauki matakin da ya dace,” inji ta.
