Gwamnatin Tinubu ta yi barazanar garƙame mahandaman shugabannin ƙananan hukumomi

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi barazanar gudanar da bincike kan shugabannin ƙananan hukumomi da su ka sauya akalan kuɗaɗen asusun ƙasafi na ƙasa (FAAC).

Antoni Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya faɗi hakan a ranar Alhamis a Abuja, yayin taron ƙungiyar Marubuta Ƴancin Ɗan-adam inda ya ce duk wanda aka samu da laifin handame ƙuɗin ƙaramar hukuma, to za a kulle shi a kurkuku.

Idan ba a manta ba, a ranar 11 ga watan Yuli ne kotun ƙoli ta yi hukuncin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi inda za su ke karɓar kuɗin kasafi kai tsaye daga asusun ƙasa.

Sannan, hukumar ta kuma ta umarci gwamantin tarayya ta riƙe ƙuɗaɗen ƙananan hukumomin da ke da shugabannin da gwamnan jiha ya naɗa ba waɗanda aka zaɓa ba.

By Babaji