Da ƊUMI-ƊUMI: DSS ta sako matasan da ta kama kan shirin zanga-zanga

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ƴan sandan farin kaya ta DSS, ta sako Injiniya Khalid Aminu da Sanusi Aliyu waɗanda ta kama su a kwanakin baya kan zargin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi wa laƙabi da ‘EndBadGovernance’.

Sanarwar haka ta fito daga Omoyele Sowere, ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar AAC a zaɓen 2023 a wani rubutu da ya yi a kafar sadarwa.

An kama Khalid ne a safiyar ranar Alhamis don zargin gayyato mutane shiga zanga-zangar gama-garin a jihar Kaduna, yayin da a irin haka aka kama Sanusi a ranar Talata a jihar Sakkwato, 23 ga watan Yuli.

Rahotanni sun bayyana cewa, an shirya zanga-zangar ne bisa la’akari da yunwa da matsanancin tattalin arziƙi a tsakanin al’umma wanda a ke sa ran gudanar da ita daga ranar 1 zuwa ranar 10 ga watan Agusta a faɗin Nijeriya.

Sai dai, hukumar DSS ta gargaɗi masu shirya zanga-zangar da cewa su dakatar da ayyukan nasu inda ta ce duk da cewa dokar ƙasa ta bada damar yin zanga-zangar lumana, sun samu bayanin shirin wasu ɓata-gari da ke ƙoƙarin yin amfani da hakan wajen tada tarzoma a Nijeriya, kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a, Peter Afunaya ya faɗa.

DSS ta ƙara da cewa, ta gano waɗanda ke bayar da gudummawa na kuɗi da masu ɗaukar nauyi da waɗanda a ke haɗa baki da su wajen cimma mummunar manufa, don haka su ke neman iyaye da masu unguwanni da cibiyoyin ilimi su shawarci ƴaƴansu, mabiyansu da ɗalibansu kan kar su kasance cikin waɗanda za a gudanar da zanga-zangar da su.

Har’ilayau, hukumar ta sha alwashin tabbatar da zaman lafiya ta hanyar aiki tare da sauran hukumomin tsaro da kuma amfani da hanyoyin da dokar ƙasa ta amince da su.

Haka kuma, rundunonin soji da na Ƴan sanda sun gargaɗi al’umma kan kar su shiga zanga-zangar tsadar rayuwa da ke tafe a faɗin ƙasar.

By Babaji