Laifina ɗaya ne a wajen Ɗangote – Shugaban NMDPRA

Spread the love

“Ba ni ke da hurumin yi wa Ɗangote abinda ya ke buƙata ba”

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Alhaji Faruk Ahmed shine Shugaban Hukumar Kula da Haƙowa da Sarrafa Ɗanyen Mai ta Nijeriya (NMDPRA). Biyo bayan tunja-tunjar da aka samu tsakanin hukumarsa da kamfanin Matatar Ɗangote, wacce ke shurin fara aiki a watan gobe, wato Agusta na 2024, inda aka zargi Gwamnatin Tarayya da cin dunduniyar matatar, Alhaji Ahmed ya yi wa Blueprint Manhaja bayanin haƙiƙanin abinda ya sani game da wannan jayayya, wacce ake fatan samun sasantawa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Injiniya Faruk Ahmad, wannan ce-ce-ku-ce da ya biyo bayana matakan da gwamnati ta fara ɗauka akan matattar mai ta Aliko Ɗangote ta kawo rigingimu da dama, asalima wasu na kallon matakin na gwamnati a matsayin ‘yar tsama tsakanin ita gwamnati da shi ko kuma it’s gwamnatin tana mass hasadda da dai sauransu. Shin ko akwai gaskiya akan wannan ko kuwa akwai abinda al’umma ba su sani ba da ya kamata a samar da su?

INJINIYA FARUK: To, a taƙaice dai ina mai shaida maka cewa, lokacin da muka ɗauki aiki anan, mun taimaka wa ita ‘refinery’ ɗin a gine-ginen da take yi. Mutanen mu suna wurin, suna taimakawa sosai. Yanzu haka zancen da nake da kai, muna da mutane guda goma da suke wurin, biyar za su shiga, idan dare ya yi, su fito, wasu biyar su shiga. Haka ake aikin a kullum. Kuma haka ake yi tun ma kan mu zo.

Shi ma Alhaji Aliko, muna magana da shi akai-akai, yana zuwa ofis ɗina, Ina kiran shi, na je can ‘refinery’ ɗin. Saboda haka abin alfahari ne a ce a Nijeriya muna da irin wannan gagarumar matattar.

Abu na biyu kuma, akwai yanayin da muka fito, ko kuma muke fuskanta, dole a ce mu yi farin ciki da wannan. Don haka yana da kyau mutane su sani ba mu da matsala da wannan aikin.

Mun yi iya kan ƙoƙari shi kansa Alhaji ya zo, kuma ya turo ‘yan uwanshi su yi mana godiya kan irin ƙoƙarin da muke masu. Don haka ba wani ƙorafi, abinda ya faru tsakanin ma’aikatanmu da ‘refinery’ ɗin ne kadai, kuma ban da shi ba wani tsakani da Allah. Duk wani zance bayan shi ana so ne kawai a ruɗar da jama’a ne.

Aliko ya kira ni, ya ce, Malam Faruk ka daina bayar da lasisi ana shigowa da kaya, kowa ya dinga siya a hannuna. Na ce Alhaji ba haka ake yi ba. Ka ga refinery ɗin ka sabuwa ce, kuma komai mataki-mataki ne. Akwai matakai har huɗu, kuma yanzu ka kai mataki na biyu. Don haka a bi abin a matakan, har akai matakin na huɗu, a gama bincike a tabbatar, a baka takarda, sai ka tafi. Ka ga a lokacin ka zama kowa kenan.

Amma shi Alhajin sai ya ce, a’a, ba haka ba, so dai ya ke in daina bada lasin. Mu kuwa wannan aikin da muke yi, amana ce aka ba mu, dole mu kare haƙƙin alumma takala ko mai kuɗi.

Abinda ya sa na ce haka, idan har muka ce a daina shigo da kaya, kuma ba inda za a samu sai nan, astagafurulla, idan har aka ce yau an samu matsala, ko cikin aikin da ba a kammala ba ya tsaya, ko za a yi gyara wani wuri, ka ga kenan ba inda za mu samu komai zai tsaya. Kuma a shigo da kaya daga waje aƙalla sai ya ɗauki kwanki 14. Wanda hakan na nufin samun matsalar mai. 

Muka nemi ya bari har Allah ya sa ya kammala, tunda dai a yanzu yana siyarwa yana samun ‘yan kuɗaɗen shiga. Amma shi ya ce, dole in daina.

Amma ka na da hurumin hana bayar da lasisi ko kuwa dokar ƙasa ce ke da wannan iko?

Ka ga bada lasin gwamnati ce ya kamata ta ce a bayar ko a daina bayarwa. Kamar dai zancen shigowa da shinkafa a lokacin Muhammadu Buhari, da ana so a taimaki manoma, sai aka ce a daina shigo da shinkafa. Ka ga sai hukuncin a lokacin ya bunƙasa harkar noma, kafin zuwan matsalar bandit.

To a wannan ɓangaren dai gwamnati ba ta ce a daina ba, domin akwai sauran ababen da ba a kammala ba a refinery ɗin. Ka ga kuwa mu ba za mu iya cewa a daina ba, tunda ba mu ke da wannan izini ba. Abu ne da har ‘yan majalisa na da baki ciki. Abu ne da sai an zauna an tattauna kansa kafin a ce a daina shi. Amma sai aka tattaro laifin aka ɗaura a kaina.

Shin ko daga ɓangaren gwamnati an kira ka don jin ta bakinka dangane da abinda ke tsakanin ka da shi Ɗangote?

To, ka ga dai ‘yan majalisa ba su kira ni sun ji ta bakina ba, kuma sun riga sun zaɓi nasu ɓangare kenan. Domin shari’a ta ce, idan irin haka ta samu, ka kira kowane ɓangare ka ji nashi. Duk da sun ce za a yi bincike, amma ka ji sun riga sun ce mu muna da laifi, ka ga sun yanke hukuncin kafin bincike. Ka ga ba zancen za mu je mu musanta ba ne, za mu je kare kai ne.

Bansan ta yadda wannan sha’ani ya koma kaina ba ni karan kaina, saboda abu ne tsakanin shi da gwamnati. Kamar yadda na faɗa a baya, lasin mataki mataki ne. A halin da ake ciki ma bai kai matakin da za a ba shi lasisin fara aiki ba, amma da ya ke refinery ɗin babba ce, kuma harka ce ta ɗan gida, shi ne aka ba shi damar fara aiki a ɓangare ɗaya. Kuma duk wannan ka-ce-na-ce da ake yi fa ma’aikatanmu na wurin suna bada taimakon da suka saba. Ka ga kuwa wannan abu rashin adalci ne ake mana, ko munafurci.

Amma takamaimai wane irin taimako ku ka yi wa Aliko Ɗangote da ya ke aiko da godiya gare ku?

Ba iya aiko saƙo na ƙaninshi, sirikanshi ko ɗan majalisa ba kawai, har shi da kanshi ya zo.

Ko zai yiwu a sanar da mutane me ya ke yi wa godiya kuma me ya sa godiyar ta goce har ake kace-nace?

Godiya ita ce, tunda aka fara gina wannan matattar muna ba shi goyon baya, duk wata amincewa da ya ke so muna ba shi cikin sauƙi. Duk wasu takardu da ya ke so muna ba shi. Duk wani lokaci da ya ke so mutanenmu su kwana, kar su je hutu, saboda a samu a ida wani aiki, mutanenmu suna wurin. Har takardar da bai tsammanin yin ta muna sanar da shi ya kamata a yi

Har ta kai muka buƙaci ya kawo mutanenshi mu koyar da su, abinda ake kira ‘workshop’. Mu koyar da su yadda za su yi komai yanda ya kamata. Mu nuna masu ƙa’idodoji da za su hana a samu matsala. Duk wannan taimako ne da muke masu, domin kamar makaho ne da ya ke neman hanya, sai Allah ya ba shi wanda zai riƙe hannunshi ya ma shi ɗan jagora.

Shin ko idan ka ga dama za ka iya bada dokar hana shigowa da kaya na mai a matsayinka na shugaban wannan hukuma da ke sa ido akan matattun mai?

A’a wannan doka ce ta gwamnati kamar yadda aka yi da dokar shigo da shinkafa, ka ga ai ba Ma’aikatar Noma ce ta saka dokar ba. Kuma ita kanta gwamnati sai da ta yi zama ta duba lamarin kafin ta amince. An duba anga ko akwai adadin manoman da za su iya bayar da abinda ake buƙata, sannan aka amince. Amma ka ga a wannan ba haka ba ne, don yanzu haka matattar ba ta iya samar da adadin abinda ake buƙata a ƙasar nan.

Amma kamar ƙorafin da aka ce ka yi kan cewa matattar ba ta samar da abinda ake buƙata, na daga ingantattun kaya, kuma tana aiki ba tare da lasisi ba. Shin me hakan ke nufi?

Kamar yadda nake magana a baya, kamar dai gina gida ne, bayan ka kammala za ka iya haɗuwa da ‘yan gyare-gyare da a yi su ba daidai ba. Ita ma haka abin ya ke, akwai ababen da ya kamata a saka bayan an kammala ta, to ba a sa ba, don haka ba zai fita yadda ya kamata ba, amma ba hakan na nufin ba ya da kyau ba, bai dai kai yadda ake buƙata ba. Amma ba kuskure ne ba, kamar ace yau kana mataki na 50, gobe ka kai 100, jibi 1000. Ka ga idan aka ce sai ya kai mataki na ƙarshe zai fara fitarwa an ƙuntata masa, don zai so ace yana samun kuɗin shiga, duk da cewa za mu iya cewa hakan.

Ya yi zargin ana yi ma sa zagon ƙasa saboda kamar yadda ya ce wasunku na da matattu a ƙasar waje ko da ku ke da alaƙa da su. Menene matsayarka kan wannan zargin da ake yi wa wasu manyan ƙasa?

Kamar yadda ka ce, NNPC ya ce, mu kuma ba NNPC ba ne, mu ‘yan doka ne, hukuma ne, mu daban muke da su, saboda haka tunda ya yi zargin NNPC, kuma shi malam Kyare ya ba shi martani, ka ga abin bai shafe mu ba.

Ko ka na ganin za a iya kai lokacin da matattun mai na Nijeriya za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da matattar mai ta Ɗangote ba tare da fuskantar wata matsala ba?

In sha Allahu kamar yadda ita NNPC suka ce, a watan nan mai shigowa matattar mai ta Fatakwal za ta fara aiki, bayan ita akwai biyu da za su biyo baya. Ka ga idan hakan ta yiwu ka ga ƙari ne, kuma duk abinda ya zama akwai zaɓi yana da amfani. To abinda muke ƙoƙari kenan ya zama ana da zaɓi. Ya zama al’umma sun samu mafita. Amma ita al’ummar ba ta fahimce mu ba, ba ta san ita muke karewa ba. Saidai da lokaci za su fahimci duk abinda muke yi saboda su muke yi

Ko akwai wani mataki da aka ɗauka a hukumace ko al’adance na zaunar da ku a tare don fahimtar inda matsalar ta ke?

Eh to, akwai wasu dattawa, iyayenmu maza da mata, sun tambaye me ya ke faruwa, kuma mun gaya masu. Wasu sun zaɓi ɓangare sun tsaya kansa. Wanda a yanzu wannan fira da muke yi da kai zai fahimtar, mutane su fahimci abinda ya ke faruwa. A ɓangaren yayenmu sun kira mu, ciki har da minista, mun yi magana, ya ce, mu daina zage-zage, kowa ya jaye ya daina magana. To amma ya kamata mutane su sani ba faɗa muke yi ba. Wallahi ba ni da wani ƙuinci game da shi, saboda abin alfahari ne gare mu, wani ya zo ya kafa irin wannan gagarumin aiki a ƙasarmu. Kuma ɗan Arewa, kuma Musulmi. ko don matsayinsa dole mu taimake shi, ko a ina ya kafa shi, matuƙar Musulmi ne ɗan Arewa, koma wane irin ne, matuƙar ɗan Nijeriya ne, dole mu yi kishin abin. 

Ba wai muna son a cigaba da siya daga Turawa ba ne, kawai dai matsayinmu ne bai kai ba na yin hakan. Idan mun kai, koda a ce ba a hana ba, su da kansu ‘yan ƙasa za su daina, saboda na cikin ƙasa ya fi arha kuma yana da kyau.

Kenan komai na tafiya daidai tsakanin ka da Aliko Ɗangote har zuwa ga lokacin da ya nemi ka hana bayar da lasisin. Shin ko ya yi ƙoƙarin ɗaga maganar zuwa sama don samun biyan buƙatar tasa ko a iya kai ya tsaya?

Gaskiya idan na ce ya ɗaga ta ko bai yi ba na yi ƙarya, don ban sani ba. Amma abinda na sani da ni da shi mun zauna mun yi magana, na ce Alhaji ka yi haƙuri, idan matattar man taka ta miƙe, za ka ga mutane da kansu ma za su zo wurin ka. Amma mu ‘yan doka ne, ya kamata a same mu da yin adalci ga kowa.

By ukarofi