Ƙungiyar ƙwararru ta ƙasa reshen Jihar Kano sun gudanar da taro don haɓaka ci gaban jihar

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Gwamnatin Jihar Kano a shirye take ta karɓi shawarwari daga ƙwararru domin haɓaka ci gaban Jihar Kano da al’ummarta.

Kwamishinan ma’aikatar ayyuka, Injiniya Marwan Ahmad  ne ya bayyana hakan a taron ƙungiyar   ƙwararu na ƙasa  reshen Jihar Kano da aka gudanar a ɗakin taro na Mambayya.

Ya ce Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ƙofar ta a buɗe yake wajen karɓar shawarwari da zai ciyar da Kano gaba daga irin wannan ƙungiyar ta ƙwararru 

Ya ce irin muhimman batutuwa da ya ji an tattauna a taron zai yi  mutuƙar taimakawa Gwamnati idan aka yi amfani da su kuma duk zai shaida wa gwamna irin abubuwa da aka tattauna a taron.

Injiniya Marwan ya ce abu ne mai muhimmanci ƙwararru su haɗu su tattauna akan abubuwa idan akwai wata matsala su jawo hankalin gwamnati akai domin ta ɗauki mataki da ya kamata,  duk kuma abinda aka nema na cigaba za su sa su a turba na tattaunawa da aiwatarwa.

Shi ma a nasa ɓangaren Injiniya Rabiu Haruna shugaban ƙungiyoyi na ƙwararru na ƙasa reshen Jihar Kano ya ce an yi taron ne domin ciyar da Kano gaba ta zama mai tasiri wajen riƙe kanta da kyakkyawan yanayi da tsaro da sana’o’i da ayyuka masu nagarta.

Ya ce ƙungiyar ta su sun yi rubuce-rubuce na jan hankalin fwamnatoci har wannan gwamnati ma sun yi rubutu akan tasirin lantarki da Kuma hanyoyi na sadarwa kuma sun ga kyakkyawan sakamako saboda zuwan Gwamna Injiniya Abba Kabir ya kafa ma’aikata ta makamashi wannan na daga abinda suka rubuta musu a lokacin shigowar wannan gwamnati.

Injiniya Rabiu Haruna ya ce sun gamsu da yadda taron nasu ya gudana duba da irin mutane ƙwararru suka halarta suka kuma yi jawabai masu muhimmancin sannan zuwan Kwamishinan  ayyuka na Jihar Kano wata nasara ce tunda ya tabbatar musu zai gabatar wa gwamna abubuwa da aka tattauna sannan ya ce su tattara bayanansu a rubuce zai sama musu dama na ganin Gwamna. 

Injiniya Rabiu Haruna ya ce Kwamishinan ya kuma ba su tabbacin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf mai sauraro ne da neman irin waɗannan shawarwari da za a ciyar da Jihar Kano gaba wannan abin a gode wa Allah ne.

By ukarofi