Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
A ƙoƙarinta na haɗa kai da AGILE don bada gudummawarsu wajen ci gaban ɓangaren ilimi a jihar Gombe, wata ƙungiyar da ba ta gwamnati ba mai suna Open Knowledge Deɓelopment Initiatiɓe ta yaba da yadda ake gudanar da aikin AGILE a Jihar Gombe.
Yabon ya fito ne daga bakin Daraktan ƙungiyar Open Knowledge Deɓelopment Initiatiɓe, Adamu Usman Garko, wanda ya jagoranci tawaga zuwa sashin gudanar da aikin a Gombe.
Adamu Garko ya ce ziyararsu ta samo asali ne sakamakon abubuwan da aka tsara a aikin da suka shafi inganta ilimin ‘yan mata matasa a jihar kuma ya tabbatar da cewa suma za su bada gudummawa wajen samun nasarar aiwatar da aikin a jihar.
Ya bayyana cewa ƙungiyar su tana shirye-shirye-shiryen horaswa, da ƙarfin gwiwar al’umma, shirin ƙarfafa mata da sauran shirye-shiryen wayar da kai da ƙarfafa gwiwa a Nijeriya.
A cikin jawabinsa kan ayyukan ƙungiyar, Sadiƙ Yahaya, ya yi bayani kan wasu daga cikin nasarorin da suka samu da kuma wasu tsare-tsaren aiki na gaba.
A cikin jawabinta, shugabar shirin na Jihar na Adolescent Girls Initiatiɓe for Learning and Empowerment (AGILE) Dakta Amina Haruna Abdul ta gode wa kungiyar bisa ziyarar da suka kai, ta kuma bayyana musu manyan sassan da suka ƙunshi aikin da kuma manufar sa na inganta ilimin ‘yan mata matasa a jihar.
Dakta Amina ta ce aikin wanda shirin Bankin Duniya ne yana kan tsarin manufofin da shirye-shiryen Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a bangaren ilimi na jihar, kuma za a fara aiwatar da manufofin sa da kyau nan ba da dadewa ba don amfanin jama’ar jihar.
Ta tabbatar da jajircewar aikin wajen wayar da kai domin isa ga dukkan al’ummomin jihar kan muhimmancin ilimin ‘ya’yan mata don tabbatar da ingantaccen rajista, dorewar karatu da kammala karatun sakandare tare da koyon sana’o’in dogaro da kai a cikin al’umma.
