Daga AISHA ASAS
Najeriya da Chana sun kulla yarjejeniyar haɗin gwiwa da nufin ƙarfafa alaƙa tsakanin masana’antun fina-finai da talabijin na ƙasashen biyu, a wani mataki da ake sa ran zai kara bude kofar musayar fina-finai da kwarewa tsakanin ɓangarorin.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne tsakanin Chana Movie Channel da Nigerian Television Authority (NTA) a Abuja ranar Juma’a, yayin taron Chana–Nigeria Film and Literature Symposium.
Yarjejeniyar ta ƙunshi shirya fina-finai tare, musayar shirye-shiryen talabijin da fina-finai, horas da kwararru, da kuma musayar fasaha.
Haka kuma, ɓangarorin biyu sun amince da faɗaɗa hanyoyin rarraba ayyukan ƙirƙire-ƙirƙire, lamarin da zai iya bai wa fina-finan Najeriya ƙarin damar isa ga masu kallo a Chana da sauran kasuwannin duniya.
Wannan haɗin gwiwa ya shafi fim da talabijin ne, amma manufarsa ta wuce samar da fina-finai kawai.
ɓangarorin biyu na son yin amfani da masana’antar ƙirƙire-ƙirƙire wajen ƙara fahimtar al’adun ƙasashen biyu da kuma ƙarfafa alaƙar Najeriya da Chana.
A ɓangaren Najeriya, yarjejeniyar na iya samar da damar samun ƙarin horo da ƙwarewa ga masu aiki a masana’antar, musamman a ɓangaren fasaha da samar da fina-finai.
A ɓangaren Chana kuma, hadin gwiwar na ƙara buɗe wata hanya ta yin mu’amala da ɗaya daga cikin manyan masana’antun fina-finai na Afirka.
