Nasarawa: Gwamna Sule ya yi ta’aziyyar rasuwar Janar Abokie

Marigayi Abokie

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Abadullahi A. Sule na jihar Nasarawa, ya miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar jiharsa, iyalai da abokan Janar Ahmed Aboki (Mai murabus) dangane da rasuwarsa.

A wata sanarwa da ta sami sa hannun gwamnan, Injiniya Sule ya bayyana marigayin a matsayin ɗan’uwa wanda ya zama abin koyi a tsakanin al’umma a halin rayuwarsa.

Kazalika, ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa wanda ya bada gudunmuwarsa ga cigaban ƙasa.

A madadin gwamnati da ma al’ummar jihar Nasarawa, Gwamna Sule ya yi ta’aziyya ga iyalai, makusanta da abokan mu’amalar marigayin bisa wannan rashi.

Kana, ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin kurakuransa, Ya sanya Jannatul Firdausi ta zama makomarsa.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*