Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya bayyana cewa, samar da na’urar zaɓe ta BVAS da hukumar zaɓe ta yi a wannan karo zai taimaka matuƙa wajen rage maguɗin zaɓe.
Ganduje ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan kaɗa ƙuri’arsa a mazaɓarsa da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ta Jihar kano.
Dokta Ganduje ya ƙara da cewa, tun daga malaman zaɓen da jami’an tsaro kowa yana ƙoƙarinsa wajen gudanar da aikinsu a wannan zaɓe.

“Cigaba da aka samu a zaɓen nan shi ne amfani da na’urar zaɓe, kuma daman shi ne mai muhimmanci, dan haka ta samu nasarar a kan wannan ƙwarai da gaske.”
