Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano
An samu disashewar Jam’iyyar NNPP a takarar ƙuri’a na mazaɓun Kankarofi da gidan makama da ke cikin birnin Kano,
Jami’in sa-ido na jam’iyyu, Mukhtar Ishak Dogarai, ya ce “babbar matsalar da muka fara fuskanta ita ce tambari (Logo) na Jam’iyyar NNPP inda ya gita dishi-dishi akwai sunan kowace jam’iyya amma babu na NNPP, kuma logon ma ya fita dishishi.”
Ya ci gaba da cewa, “inda muke ɗauko kayan zaɓen nan, wato SAS, akwai abin da babu musamman a zaɓen shugaban ƙasa yanzu haka akwai akwatu 14 waɗanda ballot paper ɗin su ba ta cika ba abin da ke faruwa kenan, amma idan muka ga abin ya yi tsamari za mu rubuta rahoto a kai” .
Da wakilinmu ya nemi jin ta bakin jami’in hulɗa jama’a na INEC a Kano, Ahmad Maulud, bai ɗaga kiran wayar da aka ui masa ba.
