Wasu ‘yan takarar siyasar Nijeriya da suka rasa rayukansu gab da zaɓen 2023

Daga AMINA YUSUF

Wasu daga cikin waɗannan ‘yan takarar ana gab da zaɓen 2023 ‘yan bindiga suka halaka su, wasu daga ciki kuma suka rasu ta hanyar wasu dalilan.

Halin rashin tsaron da ƙasar nan ya yi sanadiyyar kisan ba wai ‘yan takarar kaɗai ba har ma da masu tsaron lafiyarsu. Haka ma magoya bayansu sun sha shiga irin wannan ibtila’in a wannan kakar zaɓen.

Rahotanni dai suna nuna zargin cewa, waɗannan ‘yan siyasa vangaren da suke adawa ne da su suke kashe su saboda suna ganinsu a matsayin barazana ga siyasarsu.

Duk kuwa da cewa, a cikin ‘yan kwanakin da suka saura kafin zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar ƙasa, hukumomin tsaron ƙasar nan sun ƙara jaddada wa ‘yan Nijeriya tabbacin samun tsaro a yayin gudanar da zaɓe. Haka kuma majalisar tsaro ta ƙasa ta zauna a ƙarƙashin shugabancin Buhari inda suka nuna shiryawarsu tsaf a kan harkar tsaro a zaɓen da za a yi.

Ga wasu daga cikin ‘yan takarar da mutuwa ta cim musu ana gab da zaɓen 2023:

  1. Ɗan takarar jam’iyyar LP na Enugu ta Gabas Oyibo Chukwu: Wasu ‘yan bindiga waɗanda ba a san ko su waye ba sun bindige shi kuma sun ƙone gawarsa a ranar 22 ga watan Fabrairu, 2023. Kuma an kashe Chukwu tare da magoya bayansa su 5 a cikin mota. Al’amarin ya faru ne a yankin Amechi Awkunanaw, a ƙaramar hukumar Enugu ta Kudu. A yammacin ranar Larabar.
  2. Na biyu kuma, Christopher Elehu, ɗan jam’iyyar LP na yankin ƙaramar hukumar Onuimo, a jihar Imo, wanda a ranar 16 ga watan Disambar bara (2023) wasu ‘yan bindiga suka kutsa har gidansa suka kashe shi. Sannan suka ƙone masa gidansa kuma suka lalata masa dukiya har da mashin ɗinsa.
  3. Ɗan takarar gwamnan jihar Abiya a ƙarƙashin jamiyyar PDP, Professor Uche Ikonne shi ma ya yi mutuwar ba-zata a safiyar ranar 25 ga Janairun, 2023. A wani asibiti a Abuja. Ɗansa Dakta Uche Ikonne, ya tabbatar rasuwar mahaifin nasa bayan gajeriyar rashin lafiya.
  4. Haka shi ma ɗan takarar jamiyyar NNPP ta majalisar wakilai na mazaɓar Wudil-Garko a jihar Kano, Kamilu Ado Isa a ranar on the 21 ga Fabrairu 2023 shi ma ya ce ga garinku.

Malam Kamilu ya kasance tsohon Mataimakin Kwanturola Janar ne na hukumar NSCDC. Kuma ya rasu ne ranar Litinin ɗin da ta gabata, kwanaki kaɗan kafin zaɓe, bayan gajeriyar rashin lafiya.