Da Ɗumi-ɗumi: Atiku ya lashe zaɓe a rumfar Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, a rumfar da Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan ya jefa ƙuri’arsa, ya nuna jam’iyyar PDP tare da dan takararta na shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya doke abokin takarar sa a jam’iyyar APC, Bota Ahmed Tinubu, da tazara mai yawa.

Rumfar zaɓen wadda take a makarantar Firamaren Katuzu mai lamba 001B, inda sakamakon ya nuna dan takarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na APC ya samu kuri’u 107, yayin da Sanata Rabi’u Kwankwaso na NNPC ya samu ƙuri’u 41, sai Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP mai ƙuri’u 186.

Sakamakon Majalisar Dattawa a rumfar (001B) ya nuna jam’iyyar APC ta samu yawan ƙuri’u 301, jam’iyyar PDP 37 sai na jam’iyyar NNPP ƙuri’u biyu (2) kacal.

Haka zalika, ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai, a rumfar zaɓen, jam’iyyar PDP ce ta lashe zaɓen da yawan kuri’u 219 fiye da na jam’iyyar APC mai ƙuri’u114.

A daya ɓangaren kuma, a ɗaya rumfar zaɓen (001N-Z), a cikin makarantar Firamaren Katuzu, sakamakon shugaban ƙasa ya nuna PDP ce a kan gaba da ƙuri’u 84, fiye da APC mai ƙuri’u 52, sai NNPP mai 25. Yayin da APC ta samu ƙuri’u 155, PDP 15 a takarar kujerar Sanatan Arewacin Yobe.

Har wala yau, a takarar Majalisar Wakilai, jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 103, yayin da APC ta samu 58, NNPC kuma 5.

Har wala yau, a rumfa mai lamba 001A a cikin makarantar Firamaren Katuzu, dan takarar shugaban ƙasa, tare da jam’iyyar sa sun samu kuri’u 113, APC 94, NNPC 26, inda ɗan takarar LP ya samu kuri’u 1 kacal.

Haka kuma jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 207, PDP 24, NNPC 7 a wannan rumfar (001A) a takarar Sanatan Arewacin Yobe. Inda kuma PDP ta samu kuri’u 134, APC 89 a takarar Majalisar Wakilai a wannan rumfar.