El-Rufa’i ya koka da yadda talakawa suka ƙi fitowa zaɓe a Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Kaduna

Bayan shafe sama da sa’o’i biyar akan layin kaɗa ƙuri’a a mazaɓarsa, Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya jefa ƙuri’arsa, inda ya bayyana damuwarsa kan rashin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya da aka gudanar a jihar.

Da yake jawabi a wata hira da manema labarai a lokacin da yake jiran kaɗa ƙuri’arsa a mazaɓar PU 024 da ke Unguwan Sarki Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, gwamnan ya yi kira ga jama’a da su fito su kaɗa ƙuri’a.

Ya yabawa INEC kan inganta harkokin zaɓe, yana mai jaddada cewa “zuwa yanzu komai ya bayyana a cikin tsari a faɗin jihar; duk rahotannin da muke samu suna da kyau”.

Gwamnan ya ce, “Da safiyar yau mun samu rahoton wani lamari da ya faru a Kudancin Kaduna inda aka sace na’urar BVAS sun ƙi aiki da kuma a garin Soba inda su ma aka sace akwatunan zaɓe guda biyu”.

Yayin da yake kokawa kan rashin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a jihar, El-Rufai ya ce, “Abin da ya dame ni shi ne ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a, mutane ba sa son fitowa zaɓe. Kuma ina so in yi kira ga kowa da kowa don Allah ya fito ya kaɗa ƙuri’a, domin a cikin shekaru huɗu kuna da damar zaɓar shugabanni na gari kuma ku ɗauki abin da gaske.

Gwamna El-Rufai a cikin layin zaɓe

“Shugabannin da kuka zaɓa a yau ne za su tafiyar da al’amuran ƙasarku na tsawon shekaru huɗu masu zuwa. Don haka, don Allah kar a zauna a gida, ku fito ku yi zaɓe. Kuma ka tuna duk lokacin da ba ka fito zaɓe ba, kana ba wa mutanen da ba ka son jam’iyyarka dama, domin ƙuri’ar ka za ta rage damar zamowar wani shugaba,” inji El-Rufai.

By Editor