Masu kaɗa ƙuri’a sun koka da yadda aka warwatsa rumfunan zaɓe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Masu kaɗa ƙuri’a a yau Asabar sun koka da warwatsa rumfunan zaɓe wuri-wuri da aka yi musu na kaɗa ƙuri’a tare da bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

An samu rabe-raben rumfunan zaɓe a wasu wuraren zaɓe, amma wataƙila hukumar INEC na ganin hakan zai kawo sauƙi ga masu kaɗa ƙuri’a ne.

Wakilinmu wanda ya sa ido a kan zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya da aka gudanar a Jahi 1 da Jahi 2 a Ƙaramar Hukumar Abuja (AMAC), ya bayyana cewa masu kaɗa ƙuri’a da suka yi rajista a makarantar firamare ta Jahi 2, Jahi 2, sun rabu gida biyar a cikin Jahi kawai.

Sabbin runfunan zaɓen dai sun haɗa da Makarantar Firamare ta Jahi 2, Kasuwar Jahi 2 (Bishiyar Mango), Cibiyar Sadarwa ta Auwal, Oando ta NNPC, da Titin Yemi Osinbajo da ke kusa da Junction Gilmor, duk a gundumar Jahi.