Yadda Ganduje ya daidaita sahu wajen kaɗa ƙuri’a, ya yaba wa na’urar BVAS

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Kyamarar wakilinmu a Kano ta samu sa’ar ɗaukar Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, a lokacin da ya daidaita sahu ya bi layi kamar sauran jama’a wajen kaɗa ƙuri’arsa.

Ganduje ya jefa ƙuri’ar tasa ce a mazaɓarsa ta Cikin-gari mai lambar akwatu 008 da ke garin Ganduje, Ƙaramar Hukumar Dawakin-Tofa, Kano.

Ganduje a wajen zaɓe

Gwamnan ya yaba tare da jinjina wa hukumar zaɓe ta INEC bisa matakin yin amfani da na’urar BVAS wajen tantance masu zaɓe.

Ya ce, amfani da na’urar zai taimaka wajen damun sahihin zaɓe a Nijeriya.