Hukumar sadarwa ta Nijeriya ta bada umarnin buɗe duk wani layin waya da aka rufe a dalilin rashin haɗa shi da NIN.
‘Yan Nijeriya da yawa sun wayi gari a rufe masu layukan waya a dalilin rashin haɗa shi da NIN ɗinsu.
Sai dai a wata sanarwa da hukumar ta NCC ta fitar a ranar litinin, wanda Rueben Mauka ya sanya wa hannu ta bada umarnin duk wanda aka rufe masa layi a buɗe saboda ba a ba ‘yan Nijeriya wadataccen lokacin da za su haɗa layin nasu da lambar NIN ta su.
Sannan hukumar ta ba mutane shawara da su dage su haɗa lambar wayar su da NIN cikin lokacin da za a bayar.
