
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ya kira taron gaggawa na ƴan Majalisar.
Sanarwar kiran ta fito daga ofishin akawonsa, Chinedu Akubueze a ranar Litinin inda ya ce za a yi taron ne musamman kan ababan da ke damun ƙasa a halin yanzu.
Za a gudanar da taron ne a ranar Laraba, 31 ga watan Yuli, 2024 da misalin ƙarfe 12 na rana, kwana ɗaya kafin fara zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya.
Sanarwar ta ƙara da cewa, ana buƙatar sanatoci su yi duk shirye-shiryen da su ka dace don tattauna batutuwa masu muhimmanci ga ƙasa, majalisar ta na mai ba su haƙuri na takura da za su fuskanta game da hakan.
Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata ne Majalisa ta tafi hutun sati bakwai wanda zai ƙare a ranar 17 ga watan Satumba, 2024. Hutun ya shafi Dattijai da wakilai wanda ake yi a duk shekara.
