
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƙasashen Amurka, Birtaniya da Canada sun ankarar da al’ummar Nijeriya game yiwuwar aukuwar tashin-tashina yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da za a fara a ranar Alhamis.
Ƙasashen sun aika sakonnin ne ta mabanbanta hanyoyi inda su ka gargaɗi mutanensu da su ƙaurace wa artabu da ka iya aukuwa tsakanin jami’an tsaro da ƴan zanga-zanga, su na masu bada misali da ire-iren yadda su ka faru a baya.
Sannan, saƙonnin sun iso ne bayan da manyan ƴan kasuwa a jihohin Abuja, Sakkwato, Kano, Katsina, Ogun, Osun, Zamfara, Gombe da wasu yankunan Nijeriya su ka buƙaci a tsaurara tsaro a kasuwanni yayin gudanar da zanga-zangar.
Haka nan, a ranar 25 ga watan Yuli, rundunar ‘Yan sanda ta kira jami’anta da ke ayyukan da muhimmanci su ke mataki da ƙasa don ƙarfafa shirin zanga-zangar.
A kwanakin baya ne rundunar soji ta dakatar da ɗaukar hutu ga ma’aikatanta na wucin-gadi.
