Sufeto Janar ya umarci Rundunar ‘Yan Sanda ta bai wa ƴan zanga-zanga kariya

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Kayode Egbetokun ya umarci manyan jami’an hukumar da su bai wa ƴan zanga-zanga kariya wacce za a fara daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta.

Kayode ya faɗi hakan cikin wani saƙo da ya fitar bayan da wani babban lauyan kare ƴancin Ɗan Adam, Ebun-Olu Adegboruwa (SAN) ya nemi Sufeton ya ɗauki matakin bai wa ƴan zanga-zangar kariya.

Haka nan, Kayode ya buƙaci haɗuwa da lauyan don tattauna muhimman abubuwa kan batun inda za su gana a ranar Talata, 30 ga watan Yuli.

Zanga-zangar, wacce ta ɗauki hankalin al’umma musamman a kafafen sada zumunta, za a gudanar da ita ne a duka jihohin Nijeriya har da Abuja a watan Agusta.

By Babaji