Zanga-zanga: NYSC ta dakatar da tantancewar alawus ga ƴan hidimar ƙasa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar kula da yi wa Ƙasa hidima, NYSC ta dakatar da tantancewar biyan alawus da ‘ zaman mako-mako da ma’aikatanta da aka fi sani da ƴan bautar Ƙasa ke yi na wucin-gadi sakamakon zanga-zangar gama-gari da ake shirin gudanarwa a sassan Nijeriya.

An samu sanarwar hakan ne daga ofishin hukumar inda ta ke umurtar wakilanta na jihohi, ƙananan hukumomi da yankuna da su dakatar da ayyuka.

Hukumar ta haramta wa ƴan hidimar ƙasar shiga cikin zanga-zangar, tana mai ƙarawa da cewa za ta sanar da lokacin da za a cigaba da ayyukan tantancewar da sauransu.

Kazalika, hukumar ta haramta mu su sanya tufafin aiki a wannan satin tare da dakatawa daga gudanar da ayyukansu.

By Babaji