Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta fitar da sanarwar neman sabon kocin Flying Eagles.
Wannan sanarwa ta fito ne a shafin ta na yanar gizo, inda ta ke neman wanda zai jagorancin ƙungiyar Flying Eagles wanda sune yan ƙasa da shekaru 20.
Sanarwar ta bayyana cewa duk mai sha’awar neman aiki, dole ya zama yayi koci aƙalla na shekara biyar sannan ya saba da gasar cikin gida ta Nijeriya da kuma lasisin CAF B na koci.
Duk mai neman aiki zai iya zama ɗan Nijeriya cikin gida ko a waje. Za a rufe shafin yanar gizon neman aikin, 14 ga watan Agusta 2024
