Zanga-zanga: Ku tabbatar da tsaro a makarantu, Gwamnatin Tarayya ga shugabannin jami’o’i

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Yayin da ake cigaba da kusantar kwanakin zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya, Ministan Ilimi, Tahir Mamman, ya umarci shugabannin jami’o’i su shirya matakan kariya don bai wa makarantunsu da malamai da ɗalibai tsaro a lokacin zanga-zangar.

Sakataren hukumar kula da jami’o’i ta Ƙasa (NUC), Chris Maiyaki ya fitar da wata sanarwa a ranar Litinin, ya na mai umartar shugabannin jami’o’i su fitar da jawabai na tabbatar da tsaro ga malamai da ɗaliban makarantunsu.

Maiyaki, ya kuma shawarci ɗalibai da su kasance a cikin makarantu tare da mayar da hankali kan karatunsu domin kauce wa haɗuran da ka iya faruwa a lokacin zanga-zangar.

Gwamnatin Tarayya ta na sane da ƴancin ƴan ƙasa na yin zanga-zangar lumana, amma tare da haka, ta damu da samar da tsaro ga ma’aikata da ɗalibai da kuma ababan da jami’o’i su ka mallaka yayin da aka samu zanga-zangar da ka iya sauyawa zuwa tashin-tashina.

By Babaji