
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
An samu matsewar ababan hawa a babbar hanyar Keffi-Abuja yayin da jami’an soji su ka datse wani yanki domin gudanar da bincike kafin shiga Birnin Tarayyar Abuja.
Sojojin sun tare daidai barikin sojoji na Abacha da ke kusa da shataletalen AYA.
Kasancewar hukumomin tsaro ba su bada sanarwar hakan ba, an samu cinkoson ababan hawa wanda ya kai har gadar Nyanya, kilomita 12 kafin wajen da aka datse.
Da dama daga cikin ma’aikata da ƙananan ƴan kasuwa na Abuja da ke zama a Nyanya, Maraba, Karu da Masaka, an tilasta mu su komawa gida bayan tsawon sa’o’i a cinkoson.
Hakan na zuwa ne kwanaki uku kafin zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya da matasa ke shirin farawa daga ranar 1 ga watan Agusta.
