
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƴan bindiga sun kashe jami’in Kwastom tare da yin garkuwa da wani a harin da su ka kai sansanin hukumar a yankin Koko/Besse da ke Jihar Kebbi.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a Jihar, Tajuddeen Salisu ya ce al’amarin ya faru ne a ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa, bayan garkuwa da ɗaya jami’in, ƴan bindigar sun kuma buƙaci maƙudan kuɗaɗe domin sako shi.
Ya ƙara da cewa, an karɓi gawar jami’in da aka kashe shi ta hanyar yanka tare da kai shi Jihar Kaduna domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Kazalika, ya ce za su cigaba da bada bayanai game da halin da ake ciki, sannan su na miƙa ta’aziyyarsu ga ƴan uwa da abokan arziƙin mamacin tare da addu’o’i a gare shi.
