Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya sanya hannu kan dokar sabon mafi ƙarancin albashi

Spread the love

Shugaba Tinubu ya sanya hannu ga dokar sabon mafi ƙarancin albashi a yau. Hakan ya biyo bayan dogon tattaunawa tsakanin ƙungiyoyin Ƙwadago, gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Rahoton da Manhaja ta samu ya tabbatar Shugaba Tinubu ya sanya hannu ranar litinin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio tare da wasu ‘yan majalisun sun halarci sanya hannun domin shaida wannan gagarumin nasara.

By ukarofi