
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wasu matasa a Jihar Neja sun fito cikin gari domin zanga-zangar tsadar rayuwa da ake fama da shi a Nijeriya.
Matasan sun fito da alluna da ke ɗauke da batutuwa kamar haka; ‘Enough is Enough’, Stop ‘Anti-Masses Policies’, ‘We Are Not Slaves In Our Country’, ‘Hardship Is Unbearable’, ‘Fuel Subsidy Must Be Back’ da sauransu.
A lokacin zagayen, matasan na rera wakokin da ke nuna adawa da gwamnati.
Gwamnatin Tarayya da na jihohi sun yi ta ƙoƙarin dakatar da zanga-zangar saboda kar ɓata-gari su yi amfani da shi wajen haddasa fitina a ƙasa daga waɗanda ke ƙin demokraɗiyya.
A satin da ya gabata ne, gwamnan Jihar, Mohammed Bago ya raba wa al’ummar Neja kayan tallafi don guje wa zanga-zangar tare da yin albishir na bai wa ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomi albashin N20,000 ga kowanne su.
Ya kuma yi alkawarin bayar da buhu 50,000 na hatsi da zai taimaka wajen rage farashin kayayyakin abinci don a same su da rahusa.
Bugu da ƙari, gwamnan ya bai wa duka jagororin hukumomin tsaro mota ƙirar ‘Prado’ don tallafa wa magance matsalolin tsaro a Jihar.
Kawo yanzu, gwamnatin Jihar ko hukumomin tsaro ba su ce komai game da zanga-zangar ba.
