Yadda farashin man fetur ya kai N1,300 a jihohi

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Sakamakon bushewa da rijiyoyin man fetur da dama su ka yi, an samu layuka a gidajen mai a jihohin Kano, Legas, Kaduna, Ribas, wasu yankuna na Abuja, Nija da wasu jihohi a faɗin Nijeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa, hakan ya sa ƴan bunburutu su ke amfani da damarsu wajen sayar da duk lita ɗaya a farashin N1,300 da N1,500 a jihohin Legas da Ogun.

An fara samun yawaitar layin man ne tun ranar Asabar a jihohin inda kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPC ya ce hakan na faruwa ne sakamakon tseko da ake samu wajen ɗakko man daga rijiyoyin saboda matsalolin ƙafewa da ake fuskanta, kamar yadda jaridar ‘News Point Nigeria’ ta ruwaito.

Duk da tabbatacin shawo kan matsalolin da NNPC ya bayar, lamarin ƙara ƙamari ya ke musamman a manyan biranen ƙasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, babu motoci da aka zuba wa mai a rijiyoyin Legas a ranar Lahadi.

Wani ma’aikaci da ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya ce babu mai a kusan dukkan rijiyoyin man a ranar Lahadi wanda hakan ya sa aka samu jinkiri daga gare su.

By Babaji