NDC ta yi watsi da mutum 59 ta OK Movement, ta gargaɗi ƙungiyoyin goyon bayanta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar NDC ta nesanta kanta daga kwamitin yaƙin neman zaɓenta mai mambobi 59 da Tafiyar Obi-Kwankwaso da aka fi sani da OK Movement ta sanar da kafawa yayin tunkarar zaɓen 2027.

NDC ta yi gargaɗin cewa babu wani mutum, ɗan takara ko ƙungiyar goyon baya da ta amince wa kafa wata tawagar yaƙin neman zaɓe ko amfani da sunanta ba tare da sahalewar Kwamitin Gudanarwarta ta Ƙasa (NWC) ba.

Shugaban jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Moses Cleopas ne ya bayyana haka a wata takarda a ranar Asabar, bayan Darakta-Janar na tafiyar, John Ughulu ya gabatar da kwamitin kwanaki uku da suka gabata.

Ya bayyana cewa, jam’iyyar NDC ta koka ds jin labarin ƙafa kwamitin ba tare da amincewarta ba, don haka ta nesanta kanta da shi da kuma kira da a yi watsi da shi, yana mai cewa wajibi ne kowane ɗan takara ya kasance mai biyayya ga tsare-tsare da dokokin jam’iyyar.

Ughulu ya kuma gargaɗi mambobi da ƙungiyoyin goyon baya akan samar da tsare-tsare da ka iya rage ƙarfin ikon jam’iyyar.

Wannan na zuwa ne kwana uku bayan Obi-Kwankwaso Movement ta sanar da kafa kwamitin mambobi 59 na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ga ɗan takarar jam’iyyar, wanda ya haɗa da daraktocin shiyyoyi, masu sanya ido, masu kula da harkokin mata, tsaro, dabaru, shari’a da wasu ɓangarori.

By Babaji

Leave a Reply