NDLEA a Katsina ta kama mutane 424 ɗauke da miyagun ƙwayoyi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamandan hukumar a Katsina Sama’ila Ɗan Malam ya sanar da haka a hira da manema labarai a ofishin sa.

Ya ce waɗannan mutane da aka kama a cikin watanni shida an gurfanar da mutane 44 a kotu daga cikin su mutum 34 kotu ta hukunta kuma suna can gidajen gyaran hali.

“Haka kuma mutane 194 cikin waɗanda hukumar ta kama a kammala horo na gyara halin ka da aka saba gudanar wa na tsawon mako ɗaya,”inji Sama’ila.

Kwamandan ya bayyana cewar akwai mutane 24 da suma aka basu horo na gyara halin ka na tsawon watanni uku zuwa shida, daga cikin su mutane 16 sun kammala ɗaukan horon har sun koma wajen iyalan su.

Ya ce hukumar a Katsina ta gudanar da tarurruka na faɗakarwa akan illar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi har sau 96.

Mutane 21,565 suka halarci faɗakarwar da hukumar ta gudanar a wurare da ban da ban a faɗin jihar.

Kwamanda Sama’ila ya yaba wa gwamnatin jihar da sauran jami’an tsaro da sarakuna, ƙungiyoyin sa kai da sauran al’umma wajen ƙokarin da hukumar keyi na tsarkake jihar daga ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

By ukarofi