Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Katsina sun musanta labarai da ke fitowa daga wasu kafofin sadarwa na zamani cewa ƴan bindiga sun mamaye ƙaramar hukumar Ƙanƙara.
Mai magana da yawun ƴan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya faɗi haka a wata takardar sanarwa da ya fitar.
Ya ce wannan labari ba gaskiya bane kuma anyi shine domin saka fargaba a zukatan al’ummar ƙaramar hukumar Ƙankara da Jihar Katsina baki ɗaya.
DSP Abubakar Sadiq ya ƙara da cewa al’ummar yankin Ƙankara na zaune lafiya tare da gudanar da harkokin su na yau da kullum ba tare da alamun fargaba na rashin tsaro ba.
“Wannan labari ba shi da tushe balle makama, sharri ne aka kitsa
domin a sanya tsoro da fargaba a rayukan al’ummar ƙaramar hukumar Ƙankara da Jihar Katsina,”inji DSP Abubakar Sadiq.
Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa ‘yan sanda da haɗin gwiwa sauran jami’an tsaro a jihar suna aiki ba dare ba rana wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.
DSP Sadiq kuma yace ƴan sanda na nan na binciken daga inda labarin ya fito,kuma duk wanda aka samu da yaɗa wannan labarin ƙanzon kurege zai yabawa aya zaƙi.
Wasu kafafen sadarwa na zamani sun fitar da bayanan cewa ƴan bindiga sun mamaye yankin Ƙankara har zuwa mararraba inda takai ga har sun hana noma a yankin.
