Yajin aiki: NLC za ta tsunduma a Abuja bayan Tinubu ya ƙaddamar da ayyuka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) reshen birnin tarayya Abuja ta ce tana shirin shiga yajin aiki a yayin da Shugaba Bola Tinubu ya kammala ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a ranar 3 ga watan Yuli.

Shugabanta, Dakta Stephen Knabayi ya bayyana hakan a yayin hira da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a Abuja, ranar Alhamis.

Ya ce, za su tsunduma yajin aikin ne domin ankarar da hukumar gudanarwar birnin ta magance matsalolin da ke sa ma’aikata nazarin shiga yajin aiki.

NAN ya ruwaito cewa, an rufe ƙananan asibitoci, sannan malaman makaratun firamare suna zaune a gida, yayin da manyan ofisoshin ƙananan hukumomi shida na babban birnin suke rufe na tsawon watanni.

Lamarin ya biyo bayan rashin biya da tsarin mafi ƙarancin albashi da dokar ƙasa ta amince da shi da kuma kaso 40 na kuɗaɗen alawus.

Sauran matsalolin da ba a warware ba sun haɗa da rashin ƙaddamar da biyan ƙarin kaso 25 da 35 da Naira dubu talatin da biyar-biyar na biyan bashi da aka amince za a ba su.

Hukuncin hakan ya biyo bayan cikar wa’adin da suka bayar a zaman da aka yi da su da masu-ruwa-da-tsaki a baya na ranar 20 ga watan Yuni.

By Babaji