Shettima ya tafi Habasha ziyarar aiki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A yau Alhamis ne Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya tafi Addis Ababa, Babban Birnin ƙasar Ethiopia daga Abuja biyo bayan saƙon gayyata da Fraministan Dimukraɗiyyar Jamhuriyar Habasha, Dakta Arbiy Ali ya yi wa Nijeriya.

Kakakin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha a wata takarda, ya ce Shettima zai halarci taron ƙaddamar da shirin inganta muhalli na ‘Green Legacy Programme’.

Ya bayyana cewa, shirin za a gudanar da shi ne da nufi magance matsalolin lalata gandun daji, inganta zamantakewar tarayya da shawo kan matsalolin sauyin yanayi, lamarin da zai sa a shuka bishiyoyi guda biliyan 20 a tsawon shekaru huɗu.

Haka kuma, ya ce Shettima zai shiga tattaunawa ta musamman akan dabarun harkar noma da inganta masana’antu, waɗanda Nijeriya da Habasha suka haɗu a kai.

Ana ganin ziyarar mataimakin shugaban ƙasar za ta taimaka wajen ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu musamman akan harkokin difulomasiyya.

Sauran ɓangarorin da ƙasashen suka haɗu a kai sun haɗa da taimakon juna a ƙarfin soja, ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya da harkar tattalin arziƙi.

By Babaji