NDLEA ta rufe asusan bankin wani ƙasurgumin mai fataucin miyagun ƙwayoyi cike da biliyoyin Naira

Spread the love

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Hukumar Yaƙi da Fatauci, Sha da Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta bayyana ritsa maƙudan kuɗaɗe kimanin Naira biliyan ashirin a cikin asusan banki guda 103 na wani ƙasungumin mai fatauci da miyagun ƙwayoyi da ta cafke a kwanakin baya a birnin Legas.

Ana yi wa wanda aka yi wa zargi da aikata laifin, Mallinson Ukatu, laƙabin ɗan kasuwar Legas ma’abucin yakana.

Hukumar ta kuma shigar da tuhumce-tuhumce guda 23 akan wanda ake zargi da aikata laifukan, haɗi da kamfanonin sa guda shida masu suna ‘Fruitroprics Industries Limited, Mallinson and Partners Limited, NISPO Porcelain Company Limited, MBL Multi-links Services Limited, NISPO Oil and Gas Limited and Urban Space Services Limited’ a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja.

An shigar da tuhumce-tuhumcen ne a gaban kotun a ranar 4 ga watan Agusta na wannan shekara ta 2022, waɗanda daraktocin gabatar da ƙararraki da lamuran shara’a na kotun, J. Sunday, J. Obi, Bridget Viasimah, J. Aernan da mai gabatar ƙararraki, Mike Kassa suka rattaba hannayen su a madadin babban lauyan tarayyar Nijeriya.

Hukumar yaƙi da fatauci da miyagun ƙwayoyin tunda farko sai da ta nemi izini daga kotu na ƙwace kadarori guda 25 na wanda ake zargin sa da aikata laifukan, Mr. Ukatu wanda kuma har ila yau ake zargi sa da shigo da ƙwayoyin tiramadol cikin ƙasar nan waɗanda aka ƙiyasta su akan kuɗi Naira biliyan uku .

Wannan hamshaqin mai kuɗi dai ya yi amfani da asusun bankin UBA ne mai lamba 1006588563 na wani kamfanin sayar da kayayyakin zaƙi na ‘ya’yan itatuwa, da ya jirkita kuɗaɗe Naira miliyan 123.8 na ribar da ya samu daga haramtaccen kasuwanci.

Lamarin da ya yi bambaraƙwai da sashi na15(2)(b) na kundin laifuka, da kuma ake yi wa hukunci a ƙarƙashin sashi na15(3) da (4) na Dokar Hana zirga-zirga da kuɗaɗe ta shekarar 2011 (kamar yadda aka yi mata gyara).

By Editor