Gwamnatin Bauchi ta ƙarfafa tattalin arzikin jama’ar jihar da kimanin Naira biliyan biyu kyauta

Spread the love

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Bauchi, Alhaji Hamza Koshe Akuyam ya bayyana cewar, shirin ƙarfafa tattalin arzikin jama’a na gwamnatin jiha wato Ƙaura Economic Empowerment Programme (KEEP) ya rarraba kayayyakin sana’o’i da kuɗaɗe kimanin jimlar na biliyan biyu kyauta wa marasa ƙarfi da suka haɗa da ‘ya’yan jam’iyya da ke kan karagar mulki.

Da yake yin jawabi a taron kammala rufe bayar da tallafin ƙarfafawan a ƙaramar hukumar Bauchi wacce ta kasance ta ashirin kuma ta ƙarshe a farfajiyar filin wasan ƙwallo na tunawa da Marigayi Abubakar Tafawa Balewa (ATBS) dake garin Bauchi a kwanakin baya, shugaban jam’iyyar ya ce koda sau ɗaya, Gwamna Bala Mohammed bai tava miƙa wa kwamitinsa sunan wani mahaluƙi ba domin ya ci gajiyar shirin, lamarin da ya kwatanta da kyakkyawan shugabanci.

Koshe ya kuma lura da cewar, ɗimbin jama’ar jiha ne suka ci gajiyar wannan shiri na ƙarfafa tattalin arziki, da ya kwatanta shine irinsa na farko a cikin jihar, don haka sai ya roqi waɗanda suka ci gajiyar shirin da su alkinta abubuwa da suka samu ta yadda za ta kai su ga tsayawa bisa ƙafafunsu.

Shugaban na PDP a Jihar Bauchi sai ya kushewa ɗan takarar neman kujerar gwamna na Jam’iyyar APC, Ambasada Sadique Baba Abubakar, wanda ya bayyana da cewar, ya butulce wa jama’ar ƙaramar hukumar Bauchi, waɗanda ya ce su suka raine shi har ya zuwa abinda ya zama yau, amma kwatsam sai ya nuna shi ɗan ƙaramar hukumar Giade ne, domin kawai ya shiga takarar neman kujerar gwamnan Jihar Bauchi a zaɓen baɗi.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a bikin rufe bayar da tallafin, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya bayyana cewar, a kowane ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi guda goma sha tara da tunin aka ƙaddamar da shirin, babu wata da take da qasa da mutane 500 da suka amfana da shirin, ko mafi ƙarancin kuɗi da aka kashe da ya gaza Naira miliyan 75 ko Naira 100 a jimlace.

Ya bayyana cewar, na ƙaramar hukumar Bauchi ne ya yi bambanci inda aka raba kayayyaki sana’o’i da kuɗaɗe a jimlace na fiye da Naira miliyan 200 wa mutane kimanin 2,000 kyauta domin tayar da komaɗar tattalin arziki ko dogaro da kai.

Gwamna Bala ya ce: “Daga cikin mutane 2,000 da suka ci gajiyar shirin a ƙaramar hukumar Bauchi, guda 1,850 an ba su tsabar kuɗaɗe domin su inganta sana’o’in su, yayin da mutane 150 aka ba su kayayyakin sana’o’i da suka haɗa da motoci ƙirar bus guda uku, baburan hawa na Bajaj guda 61, kekunan ɗinki da na’urorin markaɗe ɓargaje da wasu kayayyaki sana’o’i daban-daban a matsayin ƙarfafa tattalin arziki.

Bala, wanda kuma shine Ƙauran Bauchi, kuma Jagaban Katagum, ya bayyana cewar, ba zai kasance cika baki ba idan an ce ɗaukacin jama’ar Jihar Bauchi sun amfana daga wannan tallafi na ƙarfafa tattalin arziki, la’akari da yadda lamuran tattalin arziki suka bazu ya zuwa saƙo da lungu-lungu na wannan jiha, ya ƙara da cewa a matsayin tallafin tattalin arziki kaitsaye, KEEP ya inganta rayuwar ɗimbin jama’a.

“A ƙoƙarin mu na bunqasa tattalin arzikin jama’a, haɗi da inganta da ƙarfafa jama’ar Jihar Bauchi, mun kuma duƙufa da gine-ginen sabbin kasuwanni na zamani a garuruwan Bauchi da Azare, kuma samun damar shiga wa’adin mulki na biyu, zai ƙara bamu damar faɗaɗa kasuwanni da ke cikin masarautun Dass, Ningi, Jama’are da Misau.”

By Editor