Daga CMG HAUSA
Tun daga watan Nuwamba ne, kafofin watsa labaran Afirka guda 14 suka fara nuna wasu kayatattun fina-finan ƙasar Sin guda 17 da aka fassara cikin harsunan Turanci da Faransanci da Swahili da Hausa da harshen Larabci.
Inda masu kallo daga ƙasashen na Afirka za su kalli fina-finan cikin harsunansu na gida a cikin ƙasashensu.
Babban rukunin gidan rediyo da talabijin na ƙasar Sin ne wato CMG, ya aika kunsin kyautar waɗannan fina-finai, inda za a watsa su a kafafen watsa labarai 14 na ƙasashen Afirka da suka haɗa da gidan talabijin na ƙasar Uganda da hukumar watsa labarai ta ƙasar Kenya da gidan rediyo da talabijin na Burundi da gidan talabijin na ƙasar Madagascar.
Wadannan fina-finai, za su baiwa masu kallo na ƙasashen Afirka damar kara fahimtar tunanin al’ummar Sinawa da zaman jituwa tsakanin bil-Adama da muhalli, da fadi tashi na aiki tukuru da kyakkyawar abokantaka dake tsakanin al’ummomin Sinawa da na Afirka.
Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa
