NEMA da haɗin gwiwar SEMA sun tallafa wa waɗanda iftila’in tsaro ya shafa da kayan agaji a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta ƙaddamar da rabon kayan abinci ga al’ummar da suka fito daga ƙananan hukumomi shida na jihar Katsina da suka fuskanci matsaloli daban-daban da suka shafi rashin tsaro.

Kamar yadda Manhaja ta samu, an raba tallafin ne a ranar Laraba 23 ga watan Juli, 2025 a harabar hukumar ta SEMA dake cikin birnin Katsina.

Kayan agajin sun haɗa da buhunan kayan abinci sama da 2,500, katon-katon na taliya, galalun mai na girkawa, gishiri, da katon-katon na tumatir, da sauran kayayyaki masu muhimmanci. 

Wannan shiri ne na haɗin gwiwa tsakanin NEMA da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA) don tallafawa al’ummomin da ke fama da hare-haren yan bindiga da kuma mutane masu rauni. 

Da yake jawabi a wurin taron Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda PhD CON, da ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar, Barista Abdullahi Garba Faskari, ya jaddada kudurin gwamnatocin jiha da ta tarayya na taimakon wadanda ibtila’i ya shafa. 

Gwamna Raɗɗa ya bayyana yadda gwamnatin jihar tallafawa al’ummar dake jihar a cikin shekaru biyu da suka gabata, inda ta kashe sama da N800,000,000 don sayen kayan abinci da kayan gini don rabawa jama’a. 

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin ta kuma raba ƙarin tsabar kuɗi sama da N450,000,000 ga al’ummomin da suka fuskanci matsaloli daban-daban. 

A cewarsa, fiye da mutane 3,000 da ambaliyar ruwa ta shafa sun samu tallafin kudi fiye da N180,000,000. Ya kuma sanar da cewa Gwamnatin Jihar Katsina kwanan nan ta saki sama da N200,000,000 ga hukumar bada agajin gaggawa ta jihar don siyan kayan agaji na gaggawa. 

Da take jawabi, Hajiya Zubaida Umar, Darakta-Janar ta NEMA, ta bayyana cewa ziyarar su zuwa Jihar Katsina ita ce don jajantawa al’ummomin da ke fama da fashi da makami, garkuwa da mutane, da matsalolin tsaro. 

Ta amince da tsananin matsalar a wasu kananan hukumomi kamar Musawa, Kurfi, Safana, Bakori, Sabuwa, da ƙankara, wanda hakan ya sa NEMA ta kawo tallafin abinci. 

Ta yaba da ƙoƙarin Gwamna Dikko Raɗɗa wajen magance waɗannan ƙalubale tare da ba da tabbacin ci gaba da tallafi da kayan agaji idan buƙatar hakan ta taso. 

Hajiya Binta Hussaini Dangani, Shugabar SEMA ta Jihar Katsina, ta yaba da goyon bayan da NEMA ke bayarwa akai-akai a lokutan bala’i. Ta kuma gode wa Gwamnatin Jihar Katsina bisa goyon bayan da take ba SEMA wajen gudanar da muhimman ayyukanta. 

Taron rabon kayan agajin, wanda aka gudanar a ofishin SEMA da ke Tsohon Gidan Gwamnati, Katsina, ya samu halartar shugabannin ƙananan hukumomin da abin ya shafa, wakilan iyayen ƙasa, mutane masu rauni, da sauran al’ummar yankin.

By ukarofi