Sirrin laƙani: A bar wa mai aiki aikinsa, cewar Sarkin Askar Kano

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Alhaji Muhammadu Yunusa Nabango, Sarkin askar Kano ya bayyana cewa babu wata halitta da Allah ya yi ta da babu wani dalili ko sirri, don haka ya ce masu iya magana da Larabci suke cewa laƙani gaba ya ke da ilimi (Al laƙanu fauƙal ilmu) akwai abubuwa na fasaha da Allah ya hore mana wanda da an yi waɗanda suka jahilci abun sai su kira abun tsafi ko shirka wanda kuma ba haka ba ne laƙani ne da fasaha da hikima da Allah ya ke bai wa wanda ya so domin shi ne ya ce wanda Allah ya bai wa hikima ya ba shi bai wa mai girma don haka ne za ka ga an yi wani abu wanda a iya tunanin ka da ilimin ka abin ba zai yiwu ba kuma ka ga an yi ai komai ikon Allah kuma shi ke horewa ɗan adam ya yi abin mamaki kuma ba tsafi ba kamar dai yadda sarkin askar Kano Alhaji Yunusa Nabango ya bayyana a wannan lokaci.

Haka kuma  ya ce an ce rashin jini rashin tsagawa, haka maganar take to amma akwai abubuwa wanda kana ganin ba wani abu ba ne a gunka amma masu ilimin abun muhimmin abu ne a gunsu masu ilimin abun misali kashin kada kashin awaki da ganyen ɗinɗu da wasu abubuwa idan aka haɗasu da wasu abubuwa to kaifi na aska ko ƙarfe ba zai kama mutum ba to dama kuma Allah bai yi wani abu na banza ba.

A ƙarshe ya ce a bar wa mai aiki aikinsa kuma duk abinda mutum ya gani kada ya yanke masa hukunci da jahilci da son zuciya domin hakan yana kai ɗan adam ya baro shi a harkar duniya har ma da ta lahira domin ilimi abu ne mai yawa kullum a tambayi ahalin abu domin a fita daga jahilcinsa, a cewar Sarkin Askar Kano kuma shugaban majalisar sarakunan Askan na Nijeriya.

By ukarofi